1 • GoTranscript: Shafi ne da zaka samu kudi ta hanyar sauraren sauti(audio) ko kallon bidiyo(video) kana fassarawa ko rubutawa kana dorama sautin ko kuma bidiyon wannan rubutun dakayi.
DARASI NA 1
GOTRANSCRIPT
Gameda yadda GoTranscript suka wallafa, matsakaicin mai fassara a GoTranscript yana samun N63,750 duk wata yayinda manyan masu fassara ke samun akalla N510,000 duk wata.
Idan ka zamo mai fassara a GoTranscript aikinka shine kawai ka saurari sauti ka rubutashi a cikin wurin rubutu da aka tanada, duk aikin da kayi zaka iya samun N255 a duk minti 1.
Domin zamowa memba a GoTranscript kana bukatar samun nasara akan jarabawar Gwaji da sukewa duk wanda keda ra’ayin shiga wannan manhajar.
Idan ka samu zamowa memba a koda yaushe zaka dinga ganin ayyukan-da-ke tafiya a tsarin da sukayi na aikin da aka fara sakawa aikin da za’a fara kammalawa.
Idan ka kammala aiki akwai kwararru da zasuyi duba akan aikin, idan akwai kuskure dole ka gyara sannan ka koma turawa kafin a aikawa ainihin mai aikin.
Idan kana wadannan ayyukan ana biyanka ko wane sati ta hanyar PayPal.
Duk da yake wannan aikin nada sauki amma ba irin saukin nan sosai ba, saboda wadannan sautukan zakaji wasu sautuka daga gefe masu ‘yar kwaramniya ko kuma guntuwar matsalar turanci amma ba wai ko wane sauti ba ne a haka, idan ka bincika zaka samu wadanda sautinsu yake radam.
Zaku iya ziyartar shafin ta nan: https://gotranscript.com/transcription-jobs
No comments:
Post a Comment