HANYAR DA MUTUM ZAIBI YAYI APPLY NA VERIFIED NA FACEBOOK DINSA ASAKA MASA ALAMAR TANTANCEWA (BLUE BADGE) ✅ - HAUSABLOG

Wannan shafin An kirkireshi domin koyar da Technology a yaren Hausa

People Online

Breaking

ads

Friday, 17 February 2023

HANYAR DA MUTUM ZAIBI YAYI APPLY NA VERIFIED NA FACEBOOK DINSA ASAKA MASA ALAMAR TANTANCEWA (BLUE BADGE) ✅


 HANYAR DA MUTUM ZAIBI YAYI APPLY NA VERIFIED NA FACEBOOK DINSA ASAKA MASA ALAMAR TANTANCEWA (BLUE BADGE) ✅



Assalamu Alaikum barkanmu da sake saduwa awannan shafi mai albarka.


Ayau munatafe da wata sabuwar hanyar daza kuyiwa facebook dinku verifying cikin sauki.


A yanzu ancigaba sosai wajen neman kamfanin facebook suyiwa mutum varified na page ko facebook dinsa, domin tantanceshi amma gaskiya har yanzu mutanen mu na arewa suna dauka dole yawan Followers ne yake sakawa ayiwa mutum verified to gaskiya ba haka bane, yanayin aiyukan ka ne zai saka ayi maka, da kuma yawan yin Apply na verified din. duk mai son yayi Appli din to ga yadda hanyar da zai bi.


Da farko mutum zai shiga wannan link dake kasa👇


FILL OUT THIS FORM


1) Mutum zai shiga inda aka rubutu “fill out this Form”.


2) Idan Fill out this Form ya bude mutum da farko zai zabi page zaiyiwa apply ko facebook dinsa? sai a zabi daya (masu bukatar yiwa facebook accont nasu sai su zabi facebook din).


3) Mutum zai zabi da wane lasisi zaiyi amfani wajen Apply din international passport ko National Id card.


4) Mutum zai dauko hoton International passport ko national id card.


5) Mutum zai zabi irin amfanin da yake da facebook dinsa. misali watsa labarai, ko wasanni, ko nishadi, ko kasuwanci. dss.


6) zaka zabi nigeria a matsayin Country/region dinka.


Sauran abubuwan zabi ne cikasu sai kaga dama.


7) Zakaje kayi copy na link din facebook profile dinka kayi paste nashi a inda aka saka LINK1.


8) Daga Karshe sai ka danna Alamar SEND sai ka saurari sako ta email dinka ko notification naka akan matsayin Apply dinka, idan zasuyi maka zasu gaya maka, idan bazasuyi maka ba zasu ce maka ka kara kokara apply wani wata mai zuwa.


Note:

Ba yawan Followers bane yake sawa ayi varrified na mutum ba yawan yin Apply da kuma yanayin aiyukanka a facebook sune.


Sannan wanda zaiyi Apply da International Passport zai iya samun Approving da wuri.


No comments:

ads1