YADDA MUTUM ZAI HADA VIDEO INVITITION DA WAYARSA CIKIN SAUKI - HAUSABLOG

Wannan shafin An kirkireshi domin koyar da Technology a yaren Hausa

People Online

Breaking

ads

Tuesday, 21 February 2023

YADDA MUTUM ZAI HADA VIDEO INVITITION DA WAYARSA CIKIN SAUKI

 


YADDA MUTUM ZAI HADA VIDEO INVITITION DA WAYARSA CIKIN SAUKI


Asssalamu Alaikum jama’a barkanmu da sake saduwa damu awannan shafi namu mai albarka.


Ayau zamuyi bayani akan yadda zaku hada video invitation da wayarsa batare da shan wahala.


Da farko Mutum yaje Play Store ta hanyar wannan link dake kasa ya sauke wannan application din zakuga inda akasa download now akasa nan zaku shiga domin yin download na application din.


Mutum yana Installing na Application din a kan wayarsa to sau ya bude ya fara kamar haka:


a) Daga kasa zaiga wata alamar kore sai a danna a shiga.


b) Sai a rubuta Sunan da akeso yakasance akan File din, bayan an saka sunan sai a danna “Create movie”


C) Yana dauke da abubuwa dayawa kamar haka:


“Background” zaka shiga wajen da aka saka alamar 1 sai ka zabi wace irin kala kakeso bagroung na aikinka ya kasance.

“Text” Shine rubututtuka da zakayi. Misali: Iyalan wane suna gayyatar daurin auren yayansu” haka idan zaka kara rubuwa wata jimlar zaka dawo ka taba Text dinne ka rubuta.

“Stiker” Idan akwai wani hoto karami da kakeso kasaka a gefe guda zaka iya daukoshi ka saka.

“Hand” Shine wajen da zaka zabi kalar hannun da kakeso yananyin rubutun bayan ka gama.

“Music” Shine wajen da zaka dauko waka daga cikin wakokin wayarka da zaka hada rubutunka.

wannan waje yana da matukar mahimmanci. Shine wajen da kana kan aiki duk motsi kadan kataba wajen domin zai na maka play na yadda aikinka yake tafiya.

Idan kana kan hada video Invitition dinka ko wani uzuri yazo zaka tashi, to kana taba wannan wajen domin yana saving dinsa a matsayin ajiya, duk lokacin da ka dawo zaka samu aikinka a shafin farko na app din “a”.

Shine wajen da idan kagama aikinka zakayi saving dinsa akan wayanka.

Duk wanda akwai wata tambaya ko wani abu da yashige masa Duhu zai iya tambaya ta whatsapp group dinmu

DANNA NAN KA DAUKO SHI

Note:


Akwai sauran abubuwa da mutum a hankali a hankali zai ganosu da kansa, wasu kuma zamuyi bayaninsu nan gaba insha Allah. Kowa ya jajirce ya dage yana shiga application din yayi ta jarrabawa zai koya sosai.



No comments:

ads1